Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla 23 A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Motocin da aka kona a wurin koyon sana'a dake garin Potiskum a Jihar Yobe, asabar 20 Oktoba, 2012. Ana zargin Boko Haram da kai harin
Motocin da aka kona a wurin koyon sana'a dake garin Potiskum a Jihar Yobe, asabar 20 Oktoba, 2012. Ana zargin Boko Haram da kai harin

Yayin da hukumomi suka ce sun kama wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Shu'aibu Muhammad Bama a gidan wani sanata a Maiduguri

Jami’an asibiti a Najeriya sun ce mutane akalla 23 suka mutu a wasu hare-haren da ake dora laifin kai su a kan ‘yan kungiyar Boko Haram, yayin da hukumomi suka ce sun kama wani babban jigo na kungiyar.

Jami’an asibiti sun fada yau asabar cewa an samu wadannan mace-mace ne a sanadin fashe-fashe da harbe-harben da suka faro tun shekaranjiya alhamis a yankin arewa maso gabashin kasar. Mazauna yankin sun ce an lalata gine-gine da yawa a wannan yanki da ‘yan Boko haram suka fi yawan kai hare-hare.

Jiya jumma’a da maraice kuma, jami’an sojan Najeriya sun bayar da sanarwar damke wani babban kwamandan ‘yan Boko Haram mai suna Shuaibu Muhammed Bama a gidan wani sanannen sanata a Maiduguri, sai dai ba su ambaci sunan sanatan ba.

An dora ma kungiyar alhakin mutuwar mutane fiye da dubu daya da dari biyar tun 2009. Har yanzu babu wani cikakken bayanin da ake da shi game da kungiyar, amma an yi imanin cewa kokari suke yi su shimfida yin aiki da dokokin shari’ar Islama a fadin kasar.

A farkon wannan wata ne kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce kungiyar Boko Haram ta aikata kashe kashe da cin zarafi a hare-haren da take kaiwa a kan jami’an gwamnati, da kiristoci da kuma Musulmi wadanda ba su da tsagerancin ra’ayi. Amma kungiyar mai cibiya a nan Amurka ta ce su ma dakarun gwamnatin Najeriya su na keta hakkin bil Adama da cin zarafi a yakin da suke yi da wannan kungiya.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG