Mazauna garin Potiskum a Jihar Yobe, sun ce an fara gwabzawa da misalin karfe 6 na safe. Wani gidan telebijin mai suna Channels TV yace dakarun tsaron Najeriya su na gwabzawa ne da ‘ya’yan kungiyar na ta Boko Haram.
Rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF ta fada cewa a ranar litinin da maraice ta kashe ‘yan Boko Haram su 24 ta kuma kama makamai masu yawa a birnin Maiduguri. Wata sanarwa ta ce ‘yan Boko Haram din su na buya a cikin gidajen fararen hula domin kai farmaki a kan dakarun JTF.
Shaidu sun zargi rundunar JTF da laifin cin zarafin jama’a a fadan da take yi da ‘yan Boko Haram. A makon jiya, rundunar ta musanta zargin cewa sojoji sun kashe mutane akalla 30, suka kona kantuna da gidajen jama’a a Maiduguri, a wani matakin daukar fansar wani harin bam da aka kai musu.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta fada a makon jiya cewa da alamun dukkan bangarorin sun aikata laifuffuka na cin zarafin bil Adama.