Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Ta Yamma Sun Yarda Da Girka Soja A Mali


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yana jawabi wajen bude taron kungiyar ECOWAS a kan matakan sojan da za a dauka a Mali
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yana jawabi wajen bude taron kungiyar ECOWAS a kan matakan sojan da za a dauka a Mali

Shugabannin sun amince da wannan tsarin matakan sojan kwato arewacin kasar daga 'yan kishin Islama da suka mamaye shi

Shugabannin Afirka ta Yamma, sun amince da wani tsarin matakan sojan taimakawa kasar Mali wajen kwato arewacinta daga hannun 'yan tawaye masu kishin Islama.

Shugabannin kasasxhe 15 na Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, sun amince da wannan matakin da zai kunshi sojojin Afirka su dubu 3, wanda kuma za a ba iznin aikin shekara guda.

Akasarin sojojin zasu fito ne daga kasashen dake cikin kungiyar ta ECOWAS. Tuni ma har wasunsu sun riga sun bayyana cewa zasu bayarda tallafin sojojinsu.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yace ana bukatar rundunar sojojin domin hana wanzuwar "mummunan sakamako" ba a cikin kasar Mali kawai ba, har ma da sauran kasashen Afirka baki daya.

Shugaban na Najeriya ya ce, "Daya daga cikin darussan da muka koya daga shekarun da aka yi ana fama da rikice-rikice a wannan yanki namu, shi ne mayarda duk rikicin da zai faru a wata kasa ya zamo kamar na yanki, wanda zamu taru mu hada kai mu takala. Irin wannan dabara ita ce mai nagarta a saboda rikice-rikicen da muka gani a Afirka ta Yamma a shekaru 20 da suka shige, su kan haifar da sakamakon dake bazuwa zuwa wasu kasashen da ba a nan rikicin ya samo asali ba."

Wannan tsari na kasashen Afirka ta Yamma yayi kiran da a tattauna, amma kuma yayi gargadin sai fa idan kungiyoyin 'yan tawayen zasu yi na'am da ci gaba da kasancewar Mali a zaman kasa guda wadda ke da gwamnatin tarayya wadda ba ta bin wata akidar addini.

Za a mika wannan tsarin ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya domin ya sake nazarinsa.
Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG