Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 11 Sun Mutu A Tagwayen Hare-Haren Bam


Mutane sun taru a wani wurin da bam ya tashi kan wata hanya a Kaduna, arewacin Najeriya ran 8 Afrilu, 2012.
Mutane sun taru a wani wurin da bam ya tashi kan wata hanya a Kaduna, arewacin Najeriya ran 8 Afrilu, 2012.

Rundunar sojan Najeriya ta ce wannan bam ya tashi cikin wata majami'a dake wani sansanin soja, ya kashe mutane 11, ya raunata 30.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce tagwayen hare-haren bam na kunar-bakin-wake sun ragargaza wata majami'a ta kirista 'yan darikar Protestant lahadi a wani sansanin soja, inda mutane akalla 11 suka mutu, wasu 30 suka ji rauni.

Shugaban matasa na kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Diji Haruna, ya fadawa wakiliyar Muryar Amurka Heather Murdock, cewa an kammala taron ibada a majami'ar a lokacin da bama-baman suka tashi, amma kuma limamai da 'yan kungiyar kwaya na majami'ar su na ciki a lokacin.

Mr. Haruna ya tabbatar da cewa hare-haren sun wakana ne a barikin soja na Jaji, dake Kaduna a arewacin Najeriya.

Wata majiyar soja kuma, ta ce akasarin mutanen da suka mutu, sun rasa rayukansu ne a tashin bam na biyu, a lokacin da suka je taimakawa wadanda suka ji rauni a tashin bam na farko.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma a cikin 'yan watannin baya, kungiyar nan ta Boko Haram ta kai hare-hare kan majami'u a jihar ta Kaduna.

A ranar Jumma'a, rundunar sojojin Najeriya ta gabatar da tayin bayar da tukuicin dubban daloli ga duk wadanda zasu tsegunta mata inda zata kama shugabannin kungiyar Boko Haram. Wata sanarwar rundunar ta bayyana sunayen mutane 19 da ake zargin cewa sui ne manyan wannan kungiya.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG