Mazauna wannan birni dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce sojojin sun birkice suka yi ta bude wuta a kan jama'a, a bayan da wani bam ya tashi kusa da motar sintiri na sojoji ya kashe soja akalla guda daya.
Wata sanarwar da Rundunar Tsaron Hadin Guiwa ta Najeriya ta bayar a yau laraba ta musanta wannan, tana mai cewa, "babu wata takamammiyar shaidar cewa dakarun tsaron JTF dake Jihar Borno, ta aikata kashe-kashe, ko gana azaba, ko kona dukiya ko kama mutane haka siddan."
Rundunar JTF tana yakar kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram, wadda cibiyarta ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Shaidu sun zargi dakarun tsaro da daukar matakai na rashin imani da kuma keta hakkin bil Adama.
Wani dan siyasa daga Jihar Kano dake kusa da Borno, ya fadawa Muryar Amurka bisa sharadin cewa ba za a bayyana sunansa ba, cewa rashin sanin ko wanene dan Boko Haram na bayar da wahala wajen ganowa tare da murkushe kungiyar.
Ya ce, "ba su sanya wata alama, ko wani tufafi da zai nuna cewa su 'yan Boko Haram ne."