Taron dimbin shugabannin kasashen duniya, wanda ya kasance kololuwar gangamin diflomasiya, na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Lebanon ke cewa hare-haren isra’ila sun hallaka mutane 558, 50 daga cikinsu yara kanana.
Dubban Iraniyawa ‘yan Amurka da magoya bayansu daga fadin Amurka ne suka gudanar da zanga-zanga a shelkwatar MDD dake birnin New York. Zanga-zangar wacce kungiyar gamayyar Iraniyawa ‘yan Amurka (OIAC) ta shirya ta bukaci MDD ta sa baki kan “laifuffukan da gwamnatin kasar ke aikatawa kan bil adama.
Taron kolin Majalisar Dinkin Duniyar, wanda shine matakin karshe a tsarin diflomasiya, na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Lebanon suka bayyana cewar hare-haren da Isra’ila ke kaiwa sun hallaka mutane 560 daga cikinsu yara kanana.
Ministan Tsaron Najeriya Abubakar Badaru ne ya gabatar da bukatar a taron kolin da aka yi kan makomar duniya yayin karo na 79 na babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya dake gudana a birnin New York, na Amurka.