Najeriya ta bukaci a samawa kasashen nahiyar Afrika kujerun dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
A cewar badaru, “Najeriya ta bada gudunmuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasashen duniya wajen tura dakaru da kudade da kayan aiki da kwararrun farar hula zuwa kasashen afrika irinsu, Guinea Bissau da Saliyo da Laberiya da Mali da Ivory Coast.”
Bugu da kari, Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen samarda tsaro da daidaiton al’amura a afrika ta yamma da yankin sahel,” a cewar sanarwar da daraktan yada labaran ma’aikatar tsaron Najeriya, Henshaw Oguibike ya fitar a jiya Litinin.
Don haka, Ministan ya yi kira ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniyar yayi adalci wajen baiwa nahiyar Afirka wakilci a mataki na dindindin, inda ya jaddada mahimmancin samun zaman lafiyar duniya da tafiya tare da tabbatar da tsaro da zurfafa tsarin zaman lafiyar tare da gina amana.
Badaru ya sake jaddada aniyar najeriya na tallafawa kokarin majalisar dinkin duniyar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Dandalin Mu Tattauna