Yayin da Trump da Biden za su sake karawa a zaben bana dukkansu sun tabo batun tashin hankalin 6 ga watan Janairun 2021 a yakin neman zabensu; Wasu manoma a jihar Neja dake arewacin Najeriya su na korafin cewa gwanmati ta kwace filayen su ne da karfi ba tare da diyya ba, da wasu rahotanni
A cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da dama, halin jin kai a Afganistan yana da muni. Fiye da kashi 50 cikin 100 na al'ummar kasar kimanın mutane miliyan 23.7 na bukatar agajin jin kai.
Irin gudunmuwar da wasu ‘yan gudun hijira ke bayarwa wajen kyautata rayuwar sauran mutane da ke zama a sansanonin; Bankin Duniya ya ce hada-hadar kasuwanci ta intanet ta na samar da hanyar karfafa tattalin arziki a fadin Najeriya tare da rage talauci, da wasu sauran rahotanni
Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta yi kasa ne bayan rashin nasara har sau biyu a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026.
Najeriya dai ta na fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru da dama, abin da ya haifar da kunci, wahala da damuwa a tsakanin ‘yan kasar.
'Yan takarar shugabancin Amurkan Joe Biden da Donald Trump su na ci gaba yakin neman kuri’un bakar fata a zaben dake tafe. Babban editan Muryar Amurka, Scott Stearn, ya duba yadda ‘yan takarar ke zawarcin kuri’un Amurkawa ‘yan asalin Afrika.
Domin Kari