Super Eagles ta Najeriya ta yi kasa zuwa mataki na 42 a jadawalin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta FIFA tun bayan da aka sabunta ta a ranar 4 ga watan Afrilu.
A lokacin ne, Eagles suka yi kokarin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, inda suka yi kunnen doki 1-1 da Afrika ta Kudu a ranar 7 ga watan Yuni, sannan ta sha kashi a hannun Benin da ci 1-2 a ranar 10 ga watan Yuni.
Bayan wannan koma-baya ne sabon kocinsu Finidi George ya yi murabus bayan hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta bayyana aniyar ta na daukar sabon mai ba da shawara a fannin fasaha daga kasashen waje.
A nahiyar Afirka, kasashen Morocco, Masar, da Cote d’Ivoire kowannensu ya samu tazara da mataki daya, yayin da Senegal tayi kasa da mataki daya.
Kungiyar Atlas Lions ta kasar Morocco ita ce ta daya a Afirka da mataki na 12 a jadawalin FIFA, sai Teranga Lions ta kasar Senegal a mataki na 18, Pharaohs ta Egypt da mataki na 36, kungiyar Elephants ta Cote d'Ivoire da mataki na 37, Super Eagles ce ta biyar a Afirka da mataki 38.
A cewar sanarwar da FIFA ta fitar, manyan kungiyoyi uku, sune Argentina wacce tazo ta daya (1st), inda ta rike matsayinta a jadawalin, sai Faransa a matsayi na biyu (2nd) da Belgium a matsayi na uku (3rd).
Yayinda Brazil ta hudu (4th), Ingila (5th), Portugal (6th), Netherlands (7th), Spain (8th), Croatia (9th), sai kuma Italiya (10).
Dandalin Mu Tattauna