Manyan ‘yan takara na jam’iyyu APC da PDP da sauran jam’iyyu fiye da 50 na fafatawa a neman kujerar gwamnan Kano, sai dai 'yan sanda sun kama wata mota makare da takardu da ake zargin kuri'un zabe ne.
Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na cewar zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki a jihohin biyu, yana gudana cikin sauki da kwanciyar hankali kuma ma'aikata hukumar zabe sun isa runfunan zaben kan lokaci har ma suka jira masu kada kuri’a.
A yau Laraba ne Michael Cohen, tsohon lauyan Shugaban Amurka Donald Trump, zai koma gaban 'yan kwamitin bincike na majalisar wakilan Amurka don ci gaba da bada shaida.
Wasu rahotanni sun ce Koriya ta Arewa ta sake komawa bakin aikin gina gurin gwada makami mai linzamin, a cewar wasu cibiyoyin bincike na Koriya Ta Kudu da Amurka.
Kasar Pakistan ta ce dakarunta sun harbo wasu jiragen yakin Indiya guda biyu.
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un, sun yi musayar hannu da kuma gaisawa ta jin dadi da junansu, don kaddamar da taron kolinsu karo na biyu.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar Plateau, ta gudanar da zabe a runfuna biyu dake kananan hukumomin Jos ta kudu da Riyom anan Jihar Plateau.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, sun hallaka wasu wakilan zabe a jihar Taraba.
Rahotanni daga jihar Taraba na cewa akwai wasu yankuna na kudancin jihar da ba’a gudanar da zabe ba, lamarin da ya tayar da hankulan al’ummomin yankunan.
Dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kada kuri’ar sa tare da daya daga cikin matansa Titi Atiku Abubakar, a runfar zaben.
Jam'iyyar mai mulki ta kasar Uganda ta amince da shugaban kasar Yoweri Museveni a matsayin dan takara a zabe mai zuwa na shekarar 2021.
A Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wanda ake zargi Mahamat Nour Mamadou da kasancewar dan kungiyar 'yan tawayen da ke da alaka da gwamnatin kasar ta baya-bayan nan, ya dandana kudarsa.
An samu yankewa babban madugun kwayar nan na kasar Mexico, Joaquin Guzman wanda aka fi sani da “El Chapo’ hukunci, akan laifin safarar kwaya da sauran wasu laifuka a birnin New York.
Shugaban Amurka Donald Trump zai dan dagawa kasar China kafa, indai har aka cimma matsaya akan yarjejeniyar kasuwanci.