Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai iya bari wa’adin harajin da aka sakawa kayan da ake shigowa da su daga China, idan har an kusa cimma yarjejeniya.
Harajin da Amurka ta sanya a kan kayan da ake shigowa da su daga China na dala biliyan 200, wanda aka shirya zai fara aiki ranar daya ga watan Maris, zai tashi daga kashi 10 zuwa 25 a cikin dari, har sai dai idan bangarori biyu sun cimma matsaya akan yarjejeniyar kasuwanci.
A ranar talatar data gabata Trump ya fadawa manema labarai cewa "Yanzu, idan muka kusa cimma matsaya akan wannan yarjejeniyar, zan iya ganin kaina, na dan daga musu kafa na wani dan lokaci kaɗan.”
Trump ya kara da cewa tattalin arzikin kasar China yana kasa saboda wannan rikicin harajin, yayin da baitulmalin Amurka ke ta habbaka.
Facebook Forum