Kayyaki da malaman zabe sun isa akan kari a galibin tashoshi da cibiyoyin zabe dake sassan jihar Kano.
Koda yake da fari an samu rashin fitowar jama’a sosai a wasu yankuna, amma daga bisani mutane sun ci gaba da fita domin kada kuri’a.
Kamar kowane lokacin zabe mata ne ke mamaye cibiyoyin kada kuri’a.
Koda yake zaben na gudana babu tashin hankali sosai, amma akan samun hatsaniya nan da can kamar yadda ta faru a wata tashar zabe ta Unguwa Uku.
Wani al’amari daya mamaye zaben na yau shine yadda zargin amfani da kudi tsakanin ‘yan siyasa ke kara karfi, kamar yadda wani dattijo mai suna Magaji Yalawa ke bayyana takaici akan haka.
A hannu guda kuma, Jami’ai sun kama wata mota kirar Siyana a yankunan titin ‘yan Dutse dake Magwan a birnin Kano, makare da wasu takardu da ake zargin kuri’u ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano DSP Hauruna Abdullahi wanda ya tabbatar da haka ga muryar Amurka yace motar na shalkwatar ‘yan sanda dake Bompai kuma ana ci gaba da bincike.
Da misalign karfe 10 da rabi ne gwamna Abdullahi Umar Ganduje dantakar Gwamna a jam’iyyar APC ya dangwala tasa kuri’ar a kauyen su na Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa, yayin da shi kuma takwaran sa na Jam’iyyar PDP Engr. Abba Kabir Yusuf ya dangwala tasa a Unguwar Chiranci dake karamar hukumar Gwale.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Facebook Forum