Koda yake ba a bayyana dalilin daukan wannan mataki a hukunce ba, majiyoyi sun tabbatar da cewa, ana zargin darektan na kamfanin CNPC na WAPCO da na SORAZ da bijirewa sabon tsarin da gwamnatin rikon kwarya ta bullo da shi a karkashin dokar ayyukan kamfanonin ketare dake aiki a kasar. Matakin da Bana Ibrahim na kungiyar Front Patritique ya ce ya yi dai dai.
Haka kuma ma’aikatar ministan yawon bude ido ta sanar cewa, ta janye lasisin Soluxe Hotel mallakar ‘yan China dake matsayin masauki da ofisoshi ga illahirin ‘yan China ma’aikatan man fetur a Nijar, sabada wasu tarin laifika ciki harda nuna bambanci ga ma’aikata ‘yan wasu kasashen idan aka kwatanta da albashin da ake biyan takwarorinsu ‘yan china.
China na matsayin babbar kawar Nijar a sha’anin hakar man fetur da tacewa da kuma fitar da danyen mai zuwa kasashen waje,.
Lamarin da ya sa a watan Afrilun 2024 kamfanin CNPC ya bai wa kasar rancen million 400 na dolar da za a biya da ‘danyen mai a tsawon shekara 1, to amma dangantaka ta fara tsami a tsakanin wadanan bangarorin ne, bayan da gwamnatin Nijar ta bukaci China ta bata karin wasu kudaden na daban dalili ke nan da ya sa wasu ‘yan kasa ke fassara korar darektoci ‘yan China wato a matsayin matakin huce takaici.
Tuni darektocin na China suka fice daga Nijar a jiya Alhamis, yayinda rahotanni ke cewa hukumomi sun kama asusun ajiyar bankin matatar SORAZ.
Matsalar man da ake fama da ita a yanzu haka a Nijar abu ne da ake dauka a matsayin makarkashiyar da ake zargin China da kitsawa.
Sannan matakin bai wa kamfanin kasa SONIDEP damar fara hako man fetur a rijiyoyin Koulele shi ma wani bangare ne na abubuwan da suka haddasa tauna tsakuwa a tsakanin banagorin biyu.
Saurari cikakken rahot daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna