Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Nuna Damuwa Kan Sabon Matakin Tsaron Iyaka Da Najeriya Ta Dauka


Ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare da Jakadan Najeriya a Nijar Mohammed Sanu Usman
Ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare da Jakadan Najeriya a Nijar Mohammed Sanu Usman

Ministan harkokin wajen Jamhuryar Nijer ya gayyaci Jakadan Najeriya a ofishinsa inda ya shaida masa damuwar gwamnatin Nijer kan wani sabon matakin tsaro da Najeriyar ta girke a iyakar kasashen biyu.

Girman wannan mataki ya sa Nijar bayyana fatan ganin sun tattauna da Najeriya domin tsara hanyoyin da za a yi amfani da sui a kuma hada karfi a yakin da kasashen biyu suka dukufa kansa don murkushe ta'addanci da masu aikata miyagun laifuka.

Ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare da jakadan Najeriya Mohammed Sani Usman a ganawarsu ta ranar Laraba 12 ga watan Maris, sun karkata ne kan huldar kasashen biyu a fannin tsaro na kan iyakarsu da kuma sabon matakin da Najeriya ta dauka na girke dakaru da zummar zuba ido a iyakarta.

Jami’an diflomasiyar na kasashen biyu sun yanke shawarar gaggauta bullo da wani tsarin tuntuba a tsakanin masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro game da yadda Najeriya za ta yi amfani da wannan mataki nata.

Nijar na daga cikin kasashen da suka kafa rundunar kasashen tafkin Chadi MNJTF wacce ta hada da sojojin Najeriya, na Chadi, da kamaru, da zummar yaki da Boko Haram, to amma sabanin da ya biyo bayan dambarwar juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, ya sa Nijar janye dakarunta, duk da yake ba a bayar da sanarwar ficewarta daga rundunar a hukunce ba.

Daga bisani Chadi ta janye dakarunta daga wannan runduna domin a cewarta ba da gaske a ke yin wannan yaki ba, la’akari da gibin da ficewar wadanan kasashe ta haddasa ya sa Najeriya a nata bangare ta karfafa matakai.

A wani abinda ke zama matakin bude sabon babi a huldar da ta shafi harkar tsaro a tsakanin Najeriya da Nijar hafsan hafsoshin Najeriya Janar Christopher Musa ya ziyarci Nijar a watan Agustan 2024, inda suka tattauna da takwaransa Janar Moussa Salao Barmou, sai dai har yanzu akwai alamar dari-dari a tsakanin hukumomin wadanan kasashe .

A yunkurin zuba ido kan iyakokinta, Najeriya mai fama da hare-haren ‘yan ta’addan Lakurawa ta tsaurara matakan shiga da fice ta hanyar amfani da na’urorin zamani, a yayinda ita ma Nijar a na ta gefe ta dauki mataki domin kare bututun manta sakamakon yawaitar hare-haren ta’addanci ta inda ya ratsa jihar Dosso.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Ta Nuna Damuwa Ga Sabon Matakin Tsaron Iyaka Da Najeriya Ta Dauka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG