Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Majalisar Zartaswa Ya Amince A Kashe Naira Biliyan 47 Kan Wasu Ayyuka A Najeriya


Mataimakin shugaban kasa Ya Jagoranci Taron Gwamnati FEC Da Ake Yi A Aso Rock
Mataimakin shugaban kasa Ya Jagoranci Taron Gwamnati FEC Da Ake Yi A Aso Rock

Bayanan hakan ya fito bayan kammala taron wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya jagoranta a Abuja.

A ranar Laraba ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da a kashe Naira biliyan 47 don gudanar da kwangiloli a ma’aikatun sufurin jiragen sama da na ayyuka da gidaje da kuma hukumar kwastam ta Najeriya NCS.

Bayanan hakan ya fito bayan kammala taron wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya jagoranta a Abuja.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya shaidawa manema labarai cewa an amince da takardun da ya gabatar, daga ciki akwai na sayen kayan aiki karkashin hukumar NAMA wanda za’a kashe fam €14,428,218.17 kimanin kudin Nageria N28,039,080,799.40 wajen kawo na’urorin zamani.

Sauran kwangilolin sun hada da na’urorin da za a sa a filayen tashin jirgin saman Murtala Mohammed dake jihar Legas Nnamdi Azikiwe wanda za su ci Naira biliyan 5.8.

Kazalika Mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, wanda ya yi magana a madadin ma’aikatar ilimi, ya bayyana cewa majalisar ta amince da kwangilar gina sabon ginin majalisar dattawa da zuba kayayyaki a ciki da kuma gina dakin taro da zai dauki mutane duba daya a jami’ar Abuja

Ya ce za a bayar da kwangilar ne ga kamfanin Messrs Hilkam Engineering Consultancy Ltd akan kudi N2,354,247,466.76.

A nasa bangaren Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirin kashe sama da Naira Tiriliyan 7 don gina manyan tituna 854 a fadin kasar.

Bayan haka Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya Clement Agba ya shaida cewa majalisar ta FEC ta amince a kashe N1, 554,200,000 wajen sayen wasu motoci 46 na hukumar kwastam ,Ana sa ran cewa wadannan motoci za su taimakawa hukumar kwastam wajen yi aiki da kyau.

XS
SM
MD
LG