A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja don tunawa da ranar karatu da rubutu ta duniya ta wannan shekara ta 2021, Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya yi ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su hada kai wajen taimakawa gwamnati a yakin da ta ke yi da jahilci a fadin kasar.
Adamu ya jaddada kudirin gwamnati na yaki da jahilci tsakanin mutane masu yawan shekaru, kazalika da irin himmar da ake bayarwa wajen samar da ilimi ga yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ministan ya kuma ba da tabbacin cewa mayar da hankali kan yaki da jahilci tsakanin mutane masu manyan shekaru da yara da ba sa zuwa makaranta zai yi matukar taimakawa wajen shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta.
Ya kuma bukaci da a inganta ilimin da ake samu a fannin fasahar sadarwa na zamani a kasar wadanda suka hada da rediyo, talabijin, wayoyin hannu, kwamfutoci da yanar gizo.
A cewar sa, hanyoyin za su taimaka wajen saukakawa mutane da dama samun ilimi na karatu da iya rubutu.
Ministan ya ba da misali kan cewa a shekarar 2018, akalla kashi 51.2 bisa 100 na rabin al’ummar duniya da mafi yawa daga cikinsu sun ja a shekaru, ba su taba amfani da hanyoyin sadawar na yanar gizo ba, ko ma ba su da shi gaba daya.
Don samun mafita dangane da wannan matsala da ke zama barazana ga cigaban Najeriya, Ministan ya ba da shawara a fito da wasu dabaru da za su ba da dama ga ko wanne dan kasa wajen samun ilimi mai yawa, kwarewa da iya aiki, gami da rubuce-rubuce da wadataccen ilimi na fasahar zamani.