Hukumomin sojan Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi bikin raba gari da sauran kasashen yammacin Afirka a ranar Asabar, yayin da suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kafa wata kungiya a tsakaninsu.
A ranar Lahadi ne Amurka za ta kammala janye dakarunta da kayan aikinta daga sansanin sojin sama da ke Yamai babban birnin kasar Nijar a yammacin Afirka, tare da gudanar da bikin janyewar.
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump sun gwabza muhawara a daren Alhamis, inda suka fafata kan tattalin arzikin Amurka da harkokin kasashen waje da hakkin zubar da ciki da kuma batun kaura daga kan iyakar Mexico zuwa Amurka.
Kungiyar masu aiko da rahotanni ta Fadar White House ta fada a ranar Alhamis cewa gidan talabijin na CNN ya yi watsi da bukatar baiwa wakilanta damar shiga zauren muhawarar farko ta shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Joe Biden da abokin hamayyarsa Donald Trump na jam’iyyar Republican.
Domin Kari