Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Kammala Janye Sojojinta Daga Nijar Ranar Lahadi


Sojojin Amurka a Nijer
Sojojin Amurka a Nijer

A ranar Lahadi ne Amurka za ta kammala janye dakarunta da kayan aikinta daga sansanin sojin sama da ke Yamai babban birnin kasar Nijar a yammacin Afirka, tare da gudanar da bikin janyewar.

Mataki na gaba a ajandar Amurka shi ne ficewarta daga wani sansanin jiragen yaki marasa matuki na Nijar, wanda aka shirya kammala shi a watan Agusta.

Ficewar dai ya yi daidai da wa'adin ranar 15 ga watan Satumba da hukumomin Amurka da na Nijar suka amince da shi, bayan da sabbin shugabannin sojojin Nijar suka umarci sojojin Amurka da su fice bayan juyin mulkin da aka yi a Yamai a bara.

Babban hafsan sojin saman Amurka, Manjo Janar Kenneth Ekman, ya na Nijar domin daidaita hanyoyin fita, ya shaidawa manema labarai ta hoton bidiyo cewa za a mayar da yawancin sojojin Amurka da ke Nijar zuwa kasashen Turai. Sai dai ya ce an mayar da kananan tawagogin sojojin Amurka zuwa wasu kasashen yammacin Afirka.

Yayin da Amurka ta janye wasu muhimman kayan aiki daga sansanonin a Nijar, ba ta lalata kayan aiki da kayayyakin da za a bari a baya ba. Da yake nuna fara mai kyau nan gaba, Ekman ya ce, “Manufarmu a cikin aiwatar da hukuncin shine, a bar abubuwa cikin yanayi mai kyau gwargwadon iko. Ya kara cewa “Idan muka fita muka bar ta cikin rugujewa, ko kuma muka fita ta rashin mutunci, ko kuma idan muka lalata abubuwa kamar yadda muka tafi, za mu hana zabin da kasashen biyu ke bukata na gaba. Kuma har yanzu manufofinmu na tsaro suna cikin rudani.”

Janjewar musamman daga sansanin jirage marasa matuki - wani rauni ne ga Amurka da ayyukanta na yaki da ta'addanci a yankin Sahel, babban yankin Afirka, inda masu tada kayar baya, masu alaka da al-Qaida da kungiyoyin IS ke gudanar da ayyukansu.

Ekman, wanda shi ne daraktan dabarun yaki na rundunar sojojin Amurka a Afirka, ya ce sauran kasashen Afirka da ke cikin damuwa game da barazanar ‘yan tada kayar baya da ke yankin Sahel, sun tunkari Amurka kan yadda za su hada kai da sojojin Amurka domin yakar ‘yan ta’adda. “Nijar ta taimaka mana matuka a matsayinmu na wuri saboda tana cikin Sahel kuma tana kusa da wuraren da barazanar ta fi ta'azzara,” in ji Ekman. Yanzu kalubalen zai fi wahala inji shi, domin shiga yankin sai an samu daga wajen Nijar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG