Sabon shirin CIKI DA GASKIYA za duba batun yunkurin neman gado na shanun kiwo uku da Malama Hafsatu Ahmadu ke yi a madadin ‘yan uwan ta.
Hafsatu dai da a yanzu ke zaune a jihar Neja, ta ce bayan rasuwar mahaifin su, sai mahaifiyar su ta auri wani Bawan Allah, inda shi kuma a lokacin ya kaura zuwa Mayo Ndaga a karamar hukumar Sardauna da ke tsaunin Mambilla a jihar Taraba.
Sabon mijin mahaifiyar ta su kamar yanda Hafsatu ta baiyana ya tafi da shanun ya hada su waje guda ya damka dukiyar ga dan sa mai suna Muhammad Lawal Maidabe.
Bayan rasuwar sabon mijin Hafsatu ta ce sun nemi shanun su da ta tabbatar a tsawon shekaru 47 sun karu a wajen Lawal Maidabe, amma ya yi kememe ya hana su da hakan ya kai ga kai kara har Gembu, amma ba a yi nasarar karbo shanun ba.
Domin tabbatar da an kawo karshen wannan takaddama kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, ta ce za ta shiga domin sasanta dukkan bangarorin dake takaddama da juna.
Ayi sauraro lafiya: Kashi Na Farko.
Kashi Na Biyu:
Kashi Na Uku:
Dandalin Mu Tattauna