Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya Da Gwamnatin Jihar Neja Sun Kaddamar Da Ayyukan Hanyoyi


Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello
Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello

Bankin Duniya zai kashe Dalar Amurka Milyan 60 wajan gyara Hanyoyin karkara a jihar Neja.

Bankin duniya tare da sa hannun Gwamnatin jihar Neja sun kaddamar da aikin samar da sababbabin hanyoyin yankuna karkara da yakai tsawon kilomitoci dari hudu da ukku a wadansu kauyuka guda goma sha biyu na jihar Neja.

Jagoran shirin samar da hanyoyin yankunan karkara na Najeriya wanda ake kira da RAM. Eng Uban Doma Ularamu, yace ana sa rai za’a kaddamar da wannan aikin ne zuwa karshen shekata ta 2019, inda Bankin Duniya zai kashe Dalar Amurka Milyan 60 wajan gyara Hanyoyin karkara a jihar Neja,

Bayan nan kuma Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya kaddamar da wani aikin sabuwar hanyar da Gwamnati ta yi daga kamfanin bangi zuwa Bobi.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG