Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darajar Kamfanin Apple Ta Kai Dala Tiriliyan Uku


Tambarin kamfanin Apple (AP Photo/Andy Wong)
Tambarin kamfanin Apple (AP Photo/Andy Wong)

A watan Agustan shekarar 2018, kamfanin na Apple ya taba zama na farko da darajarsa ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.

Rahotanni daga Amurka na cewa darajar kamfanin Apple ta kai dalar Amurka tiriliyan uku.

Hakan ya sa kamfanin ya zama na farko da darajarsa ta kai wadannan makudan kudade a duk fadin Amurka.

Bayanai sun yi nuni da cewa kamfanin ya dara manyan kamfanoni irinsu Walmart, Disney, Netflix, Nike, Exxon Mobil, Coca-Cola, Comcast, Morgan Stanley, McDonald’s, AT&T, Goldman Sachs, Boeing, IBM da Ford idan aka hade su wuri gudi a cewar jaridar New York Times.

Kamfanin na Apple ya faro ne a shekarar 1976. A ranar Litinin darajar kamfanin ta kai wannan adadi bayan hannun jarinsa ya kai dalar Amurka 182.01.

A watan Agustan shekarar 2018, kamfanin na Apple ya zama na farko da darajarsa ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.

Wannan ci gaba da kamfanin ya samu na zuwa cikin shekaru 42 da ya kwashe ana damawa da shi a cewar jaridar ta New York Times.

XS
SM
MD
LG