KADUNA, NIGERIA - Dama dai a can baya kungiyar Dattawan Arewacin Najeriyan ta taba kira akan shugaban kasa ya sauka daga mukamin shi, sai dai wannan karon ta ce ba shawara ta ke bayarwa ba, dole ne shugaba Muhammadu Buhari ya sauka tun da ya gaza.
Mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewacin Najeriyan Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce kasar ce ke cikin halin tsamin tsaro.
Sai dai tsohon Dan-majalissar Dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani na Jam'iyyar PDP ya ce duk da baya goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari amma bai kamata a ce ya sauka ba.
Maganar matsalar tsaro da matsin rayuwa dai na cikin manyan dalilan da masu sukar gwamnatin shugaba Buhari ke yawan bayarwa, sai dai kuma gwamnatin ta ce tana matukar kokarin kawo karshen matsalolin da ke damun wannan kasa.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti: