Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ‘Yan Jarida a Najeriya (NUJ) Ta Gargadi Mambobinta Da Su Guji Saba Ka’idar Aiki


NUJ
NUJ

A yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, kungiyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Kaduna ta ce ba za ta lamunci sabawa aikin jarida don kambama 'yan siyasa ba.

Kaduna, Nigeria - Kafafen yada labarai dai kan taka rawa wajen yada manufofin 'yan takarar kujerun siyasa da jam'iyyunsu a lokacin yakin neman zabe, sai dai kungiyar 'yan jarida reshen jihar Kaduna ta ce wajibi ne 'ya'yan kungiyar su bi ka'idojin aikin jarida wajen yada manufofin 'yan takara da jam'iyyu.

Hajiya Asma'u Halliru Yawo, ita ce shugabar kungiyar 'yan jarida ta NUJ a jihar Kaduna wacce kuma ta jagoranci shirya taron bitar, ta ce sun shirya taron ne saboda ya kamata a ja kunnen ‘yan jarida akan su guji bin ‘yan siyasa tunda su ba ‘yan siyasa ba ne, kuma a matsayinsu na shugabanni zasu horar da duk dan jaridar kungiyar da ya saba ka’idar aiki.

Tsohon mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmad Maiyaki, shi ne ya shugabanci wannan taron bita kuma ya ce dole ne 'yan jarida su yi taka-tsantsan, saboda yada labarai ba shi ne kadai aikinsu ba, suna da hakki wajen tabbatar da cewa ‘yan siyasa ba sa yaudarar al’umma.

'Yan jarida da dama ne dai su ka halarci wannan taron bita game da rawar da za su taka a lokacin zabe kuma sun ce sun amfana da taron.

'Yan jarida da yawa sukan fuskanci barazana daga wasu 'yan siyasa a lokacin yakin neman zabe, sai dai kungiyar ta NUJ ta yi alkawarin kare mutuncin mambobinta idan dai sun yi aiki kan gaskiya da kuma bin ka'idoji.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG