Ga dukkan alamu, yakin Janhuriyar Demokaradiyyar Congo na dada kazancewa duk da kokarin da ake na kira ga bangarorin da ke fadan.
Tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Falasdinawa masu marmarin komawa Gaza su dan jira a wasu kasashe har sai an sake habbaka yankin ake ta nuna shakku kan fa'idar hakan.
A ranar Litinin ne aka dakatar da ayyuka a Hukumar Tallafawa Kasashe masu tasowa ta Amurka ta USAID mai gudanar da ayyukan tallafi na biliyoyin dala ga kasashen waje.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, akwai yuwuwar Amurka ta cigaba da tallafawa Ukraine ta yin musanya da albarkatun karkashin kasar ta Ukraine.
TSAKA MAI WUYA: Cigaban Tattaunawa Kan Rikicin Cikin Gida Na Jam’iyar PDP, Fabrairu 04,2025
Wata majiyar Hamas ta shaidawa AFP cewar kungiyar na tattaunawa da masu shiga tsakani domin matsa wa Isra’ila lamba ta saki fursunoni 110 da ya kamata a saki a yau Alhamis.
Bayan da Amurka ta nuna cewa za ta janye wasu daga cikin kudaden tallafin da ta ke bayarwa a bangarori daban daban na harkokin duniya, tuni aka shiga kokawa.
An shiga cece kuce bayan da Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa wajen kawo karshen zama dan kasa ta wajen haihuwa.
A ranar Litinin Gwamnatin Donald Trump ta kori lauyoyin ma’aikatar shari’a sama da 10 da suka gabatar da laifuffuka biyu a kan shi, cewar wani jami’i, a daidai lokacin da Republican ke hanzarta tabbatar da ikon ta akan ma’aikatar.
Wasu yan Najeriya sun bayyana ra’ayin su kan shawarar da wani mai suna Chief Dokun Olumofin ya bayar cewa, a rika karɓar harajin $500 daga hannun yan Najeriya mazauna kasashen waje, a lokuttan da suka dawo gida lokacin bukukuwan Kirsimeti.
An samu wadanda ake zargin da tsabar kudi dalar Amurka dubu 400 da wani adadi na Gwal, abinda da ya daga hankali, kan irin gagarumar ta’asar da suke yi.
Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da zabar Mark Burnett a matsayin manzon Amurka a Birtaniya.
A ranar Asabar Pakistan ta ruwaito da kisan sojoji akalla 16 a yayin wata arangama da tsagerun yan bindiga a kusa da kan iyakar ta da Afghanistan.
A ranar Asabar kungiyar yan jaridun kasar Venezuela ta bayyana cewa, hukumomi a kasar sun saki wata yar jarida da aka zarga da ta’addanci, aka kuma kama ta bayan kammala sake zaben shugaba Nicolas Maduro mai cike da takaddama na watan Yuli.
Daga Isra’ilan har kungiyar ta Hezbollah da Iran ke marawa baya na fuskantar caccaka game da karya alkawarin yarjejeniyar zaman lafiya da ta fara aiki a ranar 27 ga watan Nuwamba, da nufin kawo karshen yakin da ake yi.
A Ranar Lahadi dantakarar jam’iyar New Patriotic Party mai mulki a Ghana, mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasar.
kasashen gabashin Afrika sun sake yin wani hubbasa kan batun samun zaman lafiya a gabashin Congo, duk da dai ana ganin bukatar tasu na da rauni.
A ranar Asabar zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar aza harajin kashi 100 kan gungun kasashen BRICS 9 muddin suka yi gigin yin kafar angulu ga dalar Amurka.
Yan gudun hijiran Rohingha sama da 100 da suka hada da mata da yara ne aka ceto, bayan da jirgin ruwan su ya nutse a ruwan Indonesiya.
Domin Kari