Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Donald Trump Ta Kori Wasu Lauyoyin Ma'aikatar Shari’a Daga Aiki


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A ranar Litinin Gwamnatin Donald Trump ta kori lauyoyin ma’aikatar shari’a  sama da 10  da suka gabatar da laifuffuka biyu a kan shi, cewar wani jami’i, a daidai lokacin da Republican ke hanzarta tabbatar da ikon ta akan ma’aikatar.

An kori jami’an ne bayan da mukaddashin babban mai shari’a James McHenry, wani wanda Trump ya zaba, ya yanke hukuncin cewa, ba za’a iya daukar su matsayin amintattau ba, sakamakon muhimmiyar rawar da suka taka wajen hukunta shugaban kasar, cewar wani jami’in hukumar sharia.

McHenry ya buga misali da karfin ikon da Trump ke da shi a karkashin kundin tsarin mulkin Amurka, domin tabbatar da korar, kamar yadda bugun takardar sallamar da kafar labarum Reuters ta gani, ta bayyana.

Lauyoyin sun yi aiki da lauya na musamman Jack Smith, wanda ya jagoranci masu gabatar da kara na tarayya su biyu na hukuncin da aka yankewa Trump, da ma’aikatar shari’ar ta yi watsi da su bayan zaben shi a watan Nuwamba. A farkon watan nan Smith ya ajiye aiki a ma’aikatar shari’ar.

Barin aikin lauyoyin ya girgiza mutane, ganin cewa a bisa al’ada lauyoyi kan cigaba da aiki a bangaren shari’ar a shugabancin ko wacce gwamnati, ba tare da an ladabtar dasu ba sakamakon wata rawa da suka taka, a yayin gudanar da wani muhimmin bincike. Korar dai ta fara aiki ne a nan take.

Labarin korar ya zo ne rana guda da Ed Martin, babban mai gabatar da kara na tarayya a Washington wanda Trump ya nada ya bude sake nazari kan tuhume tuhumen da akewa mutanen da aka zarga da taka rawa a harin ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2021 kan majalisar dokokin Amurka, cewar wani da ke da masaniya akan batun.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG