Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Yan Gudun Hijirar Rohingha Daga Teku Akan Hanyar Su Ta Zuwa Indonesiya


Wasu yan gudun hijira da jirgin su ya nutse a ruwa
Wasu yan gudun hijira da jirgin su ya nutse a ruwa

Yan gudun hijiran Rohingha sama da 100 da suka hada da mata da yara ne aka ceto, bayan da jirgin ruwan su ya nutse a ruwan Indonesiya.

Yan gudun hijiran Rohingha sama da 100 da suka hada da mata da yara ne aka ceto, bayan da jirgin ruwan su ya nutse a ruwan Indonesiya, cewar hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Asabar.

Mafi yawan kabilar Rohingha musulmi na fuskantar gagarumar tozarta a Myanmar, inda dubbai ke kasada da rayuwar su a duk shekara, tayin doguwar tafiya ta ruwa, mai cike da hadurra zuwa kasashen Malaysiya ko Indonesiya.

Faisal Abdul-Rahman na hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ya shaidawa kafar labaran AFP a ranar Asabar cewa, sun karbi rahoto daga gwamnatin gabashin Aceh da yace, yawan yan gudun hijiran ya kai 116.

Yace, har yanzu yan gudun hijiran na nan a gabar kogin, ba a kuma yanke shawarar inda za’a kai su ba.

Ya kara da cewa, an samu jirgin ruwan na rubabben katako da ke dauke da yan Rohinghan a daidai lokacin da rabin shi ya nutse cikin ruwa, nesa kadan daga Arewa maso gabas na gabar ruwan tsibirin Sumatra

Wani mai kamun kifi a yankin, Saifudin Taher yace, an fara hango jirgin ruwan na shiga yankin ruwan gabashin Aceh a ranar Asabar da safe, inda sa’oi kadan daganan ya kusa nutsewa cikin ruwa.

Duk pasinjojin dai sun tsira da ran su, to amma mutum guda daga ciki ba shi da lafiya, inda anan take aka yi mishi magani, kamar yadda Saifudin ya shaidawa kafar labarum AFP, ya kara da cewa, tsakanin jirgin da gabar ruwan nisan mita 100 ne kacal, yadda yan gudun hijiran za su iya takawa da kafar su zuwa tudun mun tsira.

Zuwan yan Rohinghan kasar Indonesiya na neman zama wani salo na faruwar hakan akai akai ko a jere, da kan lafa a lokacin watannin iska mai karfi, ya kuma cigaba da zaran yanayi ya lafa a teku.

Ko a watan da ya gabata yan gudun hijiran Rohingha su 152 ne aka tsamo zuwa gabar ruwa, bayan shafe kwanaki ba duriyar su da ga yankin ruwan kudancin Aceh, inda jami’ai su ka yi shawarar barin su su taka kasa.

Kasar Indonesiya ba ta cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yangudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, don haka tace, ba za’a iya tursasa ta ta karbi yan gudun hijira da ga Myanmar ba, inda tayi kiran da maimakon haka, kamata yayi makwabtan kasashe su dauki nasu kason na nauyin kula da ba yan Rohinghan masauki.

Da dama daga yan kasar na cike da sanin irin bakar wahalar da su kan su suka sha a gwamman shekarun da aka kwashe na zubar da jinni a rikice rikicen da suka rika fama da su, don haka suna tausayawa yan Rohinghan a matsayin su na musulmi yan uwan su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG