Wasu ‘yan kasar na ganin wannan nadin na zuwa ne a kurarren lokaci kamar yadda Usman Ma’azu ke cewa.
Sai dai ministan sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce kafin a fara aikin sai da aka biya diyyar dukkan gonakin da aikin ya ratsa ta cikin su.
“Ya zama wajibi a tashi tsaye a kawar da su ('yan bindiga,) domin kuwa sun zama wata babbar barazana ga rayuwar jama’a da makomar kasa baki daya.
Da aka tuntubi rundunar ‘Yan-sandan jihar Zamfara akan wannan batu, Kakakinta DSP Shehu Muhammad ya ce zai bincika.
Hukumomin Najeriya dai sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalar ta tsaro a sassan kasar musamman a arewa maso yammaci da gabashi.
Wani sabon rikici tsakanin al’ummomin Tibi da Fulani a kananan hukumomin Lafiya da Obi a jihar Nasarawa, ya yi sanadin rasa rayuka da dama.
“Muhimmancin wannan taro shi ne don a hada kai tsakaninmu da su, don a ci moriyar irin ci gaban da Turkiyya take samu," in ji Garba Shehu.
"An samu nasarori a Najeriya bayan da kasar ta koma tafarkin dimokradiyya kusan shekaru 20 da suka gabata, amma samar da yanayin da ke tabbatar da walwala da sauran muradu ga ‘yan kasa ya samu koma baya a baya bayan nan."
Zanen Ibe na dauke ne da hoton mahaifar mace mai ciki kuma bakar fata- irin hoton da ba’a cika gani ba a zane-zanen sha'anin kiwon lafiya.
Wani mai Shari’a babbar kotun Pietermaritzburg a lardin mahaifar tsohon shugaba na KwaZulu-Natal, ya dage sauararan karar tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma zuwa 10 ga watan Agusta.
Ma’aikatar ayyukan hajji ta ba dukan mata izinin gudanar da ayyukan haji ta tare da Mehrem ba, idan zasu tafi cikin gungun ‘yan’uwansu mata.
Gwamnatin Habasha ta ayyana tsagaita wuta a yankin Tigray, yayinda tsohuwar jam’iyar da ke mulki a kasar da dakarunta suka shiga Mekelle babban birnin yankin.
An umarci tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya shafe watanni goma sha biyar a gidan yari bayan kin bayyana gaban kwamitin dake gudanar da bincike kan jerin zargin cin hanci da rashawa da aka tafka lokacin da ya ke shugaban kasa.