Kungiyar Islamic Relief Organization da kungiyar Smile Mission sunyi wa masu jinyan ciwon ido tiyata kyauta a Maiduguri
Wata madatsar ruwa a wani kwazazzabo dake kasar Kenya ya goce a daren jiya, inda ya kashe mutane akala 27.
Dakarun Isra'ila sun ce sun maida hankali ne a hare haren da aka kai da jiragen sama kan cibiyoyin ayyukan leken asiri, cibiyoyin da ake ajiyar makamai da motocin yaki, kuma jiragen sun tarwatsa na'urorin da Syria ke amfani dasu domin kariya.
Bikin nadin sarautar sarkin Tsibiri, bayan jayayya game da zaben sarkin da masu hamayya da shi suka yi ta yi harda da kai kara kotu.
Taron yan darikar Tijjaniyya a Najeriya yayin da watan Ramadan ke nan tafe, Afrilu, 5, 2018
Jama'a sun taru a wani wurin shirye-shirye gabanin fara azumin watan Ramadan
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osibanjo ya kai ziyara makarantar firamari a Akure dake jihar Ondo domin binciken shirin ciyar da dalibai da aka fara a makarantar inda Gwamnan Ondo Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu da wasu ministoci suke cikin tawagar ziyarar.
Wani bincike da cibiyar nazarin harkokin Afrika -ACSS-ta yi fa arkon wannan shekarar ya gano cewa, kasa da kashi 40 cikin 100 na kasashen Afrika suke aiwatar da wa'adin mulkin da kundin tsarin mulkin kasa ya kayyade.
Cibiyar Red Cross ta ce an sace ma'aikaciyarta da misalin karfe 8 a daren jiya Laraba yayin da wadansu mutane dauke da bindiga suka shiga filin ofishin a Mogadishu.
A cikin makonnin nan, muhawara ta kara zafafawa biyo bayan barazanar da Trump yayi na sanyawa kayayyakin China tarar dala biliyan 50 domin ladabtar da Beijing kan abin da gwamnati ta kira rashin adalcin a tsare tsarenta na harkokin cinikayya.
Wani rahoto da aka fitar na shekara da kungiyar yan jarida ta Reporters without boarders ta wallafa, na nuni da cewa cin zarafin yan jarida da ake yi na cigaba da karuwa, ba kawai a kasashen da ake mulkin mallaka ba.
Yayin da alkaluman mutanen da suka mutu a tagwayen harin kunar bakin wake da aka kai garin Mubi ke karuwa, yanzu haka an garzaya da wadanda ke da munanan raunuka zuwa cibiyar lafiya dake fadar jihar wato FMC Yola.
'Yan yankin kudu maso gabashin Najeriya mazauna Amurka, wadanda ke son a raba Najeriya su koma Biafra, na zanga zanga a wajen fadar shugaban Amurka da kan zuwan shugabn Najeria Muhamadu Buhari birnin Washington DC.
Hukumar Kwastam tayi kira ga mazaunan da ke kan iyakokin Najeria da su baiwa hukumar hadin kai wajen dakile harkokin yan fasakwauri a kasar, inda ta bayan cewa ta kama haramtattun kayan fasakwauri na Naira Biliyan 12.
Shugabanin Afrika da ministoci a wurin bude taron tattaunawa na 4 da ake yi duk shekara kan shaidar zama yan kasa
An bada horo ga humomin karkara na jahohi 8 a Nijer da kungiyar PAK TURWA Nijer ta shirya yau a garin Birnin Konni.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ya kai ziyara makarantar frimary a Gwarinpa, Abuja inda yayi wa daliban makarantar frimary karatu domin tunawa da ranar litafi ta duniya inda ministan tarraya da ministan ilimi suka yi masa rakiya.
An kawo karshen taron manyan hafsoshin sojojin Afrika a Najeriya wanda rudunar sojan Amurka ta shirya da zummar kawo karshen matsalar tsaro a Nahiyar.
Domin Kari