Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace wata Ma'akaciyar Jinya A Mogadishu Babban Birnin Somaliya


Cibiyar Red Cross ta ce an sace ma'aikaciyarta da misalin karfe 8 a daren jiya Laraba yayin da wadansu mutane dauke da bindiga suka shiga filin ofishin a Mogadishu.

Kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ta tabbatar da sace wata ma'aikaciyar jinya da ke aiki da kungiyar a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

"Muna cikin damuwa matuka kan tsaron abokiyar aikin mu", inji wata rubuttaciyar sanarwa da Daniel O’Malley, mataimakin shugaban kungiyar Red Cross a Somaliya ya rubuta. Yace " Mai Jinya ce wacce take aiki kullum domin ceto rayuwa da inganta lafiyar 'yan kasar Somaliya dake cikin hadari."

Kakakin hukumar tsaron Somaliya, Abdulaziz Ali Ibrahim, ya shaidawa VOA cewa an sace matar ne a filin ofishin cibiyar agajin ta Red Cross.Ibrahim yace matar yar kasar Jamus ce mai suna Sonja Nientiet.

Kungiyar agajin tana amfani da masu tsaro dake zaman kansu. Makwabta sun ce basu ji wata hatsaniya ko harbe harben bindiga daga ofishin.Cibiyra ta Red Cross tace tana aiki da jami’ai domin kokarin a sako ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG