Hukumar Kwastan ta Najeriya ta kama haramtattun kayan fasakwauri na kimanin Naira Biliyan 12 a yan watannanin baya akan iyakan Najeriya da Jamhuriyar Benin.
A wani taron da hukumar kwastam ta gudanar a yankin Seme ta bayana kayakin da ta kama da suka hada da kajin kankara, da buhunan shinkafa da kayyakin atamfofi da shaddodi. Hukumar tayi kira ga mazauna kan iyakokin Najeriya da su cigaba da baiwa hukumar gudumuwar da ya dace wajen dakile harkokin yan fasakwauri a kasar.
Kwantrola Muhammad Jibril ya bayyana cewa an hana shigowa da shinkafa ta iyaka sai ta tashar ruwa, ya kara da cewa manyan motocin da ke dauko shinkafa basa bin hanyar Seme inda ya bayyana cewa shinkafar da suke kamawa ta kananan motoci ake shigowa da su.
Hukumar Kwastam ta dauki matakai na fitar da man fetur daga Najeriya zuwa manyan kasashe, wanda hukumar ta ce tana taimakawa zagon kasa wajen tattalain arziki da kuma haifar da karancin man fetur a Najeriya.
Facebook Forum