Taron na wannan shekara ya banbanta da yadda aka saba gani a shekarun baya, inda dubban mutane ke halartar wannan taro dake tattaro shugabannin kasashe da firai ministoci da manyan tawagogi da kuma wakilai na kungiyoyi masu zaman kansu zuwa nan birnin New York.
Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani tare da mataimakinsa da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin sa, sun bar kasar yau Lahadi, lamarin da ya bai wa mayakan Taliban dama su sake komawa kan mulki bayan shekara 20 da sojojin da Amurka ke wa jagoranci suka hambarar da su daga kan karagar mulki.
Jami’ai a kasar Kamaru sun ce da alama mayakan Boko Haram sun sauya dabarun su, inda a yanzu suke kai hari kawai kan sojojin da wuraren gwamnati a kokarin da su ke yi na janyo daukan wasu da dama.
A lokacin babbar sallah, Musulmai a fadin duniya suna yin hadaya, wato yanka dabbobi domin yin sadaka domin neman lada daga wurin Allah. Wasu ma’aikatan Sashin Hausa na Muryar Amurka sun yi takakkiya zuwa Pennsylvania domin gabatar da wannan ibada.
Wasu ‘yan kasar Colombia da ‘yan sandan kasar Haiti suka tsare dangane da kisan gillar shugaban kasar Jovenel Moise sun halarci shirye-shirye na horo da karatu na sojojin Amurka, kamar yadda kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya tabbatar a cikin wata sanarwa da aka aikawa VOA.
Jami’ai a kasar Haiti sun fada daren jiya Alhamis cewa fiye da mutane 12 ne ke tsare dangane da kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Haiti Jovenel Moise.
Sudan ta Kudu ta cika shekara 10 da samun yanci kai yau Jumma’a sai dai babu wani abin kirki da za a yi murna a kasar da yakin basasa ya durkusar inda ake fama da rashin kwanciyar hankali na yau da kullum da kuma matsananciyar yunwa.
Shugaban 'yan sandan kasar Haiti ya ce an kashe mutane hudu da ake zargi da kisan shugaba Jovenel Moise jiya Laraba a wata musayar wuta da ‘yan sanda.
An sami kamfanin Donald Trump da kuma babban jami’i mai kula da harkokin kudinsa da laifukan da suka samo asali daga masu bincike na New York kan harkokin kasuwancin tsohon shugaban kasar.
Domin Kari