Bayanin ya fito fili ne yayin da ake nazarin runbunan adana bayanan horaswa, Laftanar Kanal Ken Hoffman ya fada, ba tare da bayyana lokacin da kuma wurin da aka yi horon ba.
Hoffman ya ce muna ci gaba da yin nazari, don haka ba mu da wani karin bayani a wannan lokaci. Jaridar Washington Post ce ta fara bada rahoton ci gaban.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ce tana horasda dubban sojojin daga Kudanci da Tsakiyar Nahiyar Amurka da yankin Caribbean kowace shekara.
Hoffman ya ce horon yana maida hankali ne kan mutunta ‘yancin dan adam da bin doka da kuma sojojin wadanda ke karkashin jagoranci farar hula da aka zaba.
Jiya Alhamis, shugaban kasar Colombia ya fada wa wani gidan rediyon kasar cewa yawancin ‘yan Colombia da ake tsare da su an yaudare su ne da tunanin za su samar da aikin kare tsaron lafiyar shugaban kasar Haiti.