A tsakiyar daren ranar 9 ga watan Yulin 2011, shagulgulan biki ya barke yayin da aka haifi sabuwar kasar a duniya kuma mutanan Sudan ta Kudu sun yi murnar ganin karshen gwagwarmayar shekara goma na neman kasa daga Sudan.
Bayan Shekaru biyu, Sudan ta Kudu ta kasance cikin yaki, aka manta da aikin gina kasa, yayin da wadanda suka yantar daita suka wargaza kasar, wanda suka yi fatali da babban cigaban da ake fata na samun zaman lafiya da ci gaba a nan gaba.
Kusan mutum dubu 400,000 ne suka mutu kafin a ayyana tsagaita wuta a 2018, amma kasar ta yi ta fadi tashi don hadewa kuma yafi rauni fiye da ko wane lokaci da fuskantar yunwa da rashin tsaro na siyasa da lalacewar tattalin arziki da kuma bala’o’i na kasa.