Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta ayyana tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, a matsayin wanda ya lashe zaben gwanan jihar Imo.
Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ce an maido da zaman lafiya a garin Izzi, bayan barkewar wani rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da PDP a farkon wannan makon, wanda ya yi sanadiyar kone wasu gidaje, da asarar dukiyoyi.
Dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasa da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi, yanzu ya janyo fushi daga masu ruwa da tsaki da kuma sauran al'ummar kudu maso gabashin Najeriya.
An sako wasu limaman addinin kirista da akayi garkuwa dasu tun a makon da ya gabata.
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Imo ta kama wasu mutane biyu dauke da bam a garin Orlu, dake yammacin jihar, yayin da ake zargin zasu wani bangaren garin ne domin su tada shi.
Akwai alamun cewa umurnin hana fita da kungiyar ‘yan awaren Biyafara ta IPOB ta ayyana a duk fadin yankin kudu maso gabashin Najeriya, bata yi tasiri ba yayin da harkoki ke ci gaba da tafiya kamar yadda suke a yawancin manyan biranen yankin. ciki har da Awka, babban birnin jihar Anambara.
A jihar Imo, an samu rarrabuwar kawuna akan umurnin hana fita a ranar Juma’a, 14 ga wannan watan, wanda kungiyar ‘yan awaren Biafra ta IPOB ta ayyana a duk fadin yankin kudu maso gabas, don nuna fushi akan bacewar madugun kungiyar, Mista Nnamdi Kanu. da kuma iyayensa, wadanda har yanzu, ba’a gano inda suke ba.
Gwamnatin tarayyar kasar na dab da kammala gyare-gyare akan hanyar Okigwe ta Arondizuogu zuwa garin Akokwa wacce ta dade da lalacewa, da nufin bunkasa kasuwanci a fadin yankin kudu-maso-gabashin Najeriya,
Ranar 23 ga watan Agusta, rana ce da majalisar dinkin duniya ta kebe don tunawa da cinikin bayi da haramtashi a fadin duniya. Da yake hira da Muryar Amurka yau akan muhimmancin wannan ranar, Dakta Ogbonna Onuoha na jami’ar jihar Abia dake garin Uturu, ya ce duk da cewa tun karni na 19 ne majalisar Burtaniya ta haramta cinikin bayi, har yanzu ana ci gaba da bautar da mutane a sassan duniya daban daban.
Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mayar da martani, dangane da wadansu sharrudan da kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB ta gindaya mata da gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya.
Farashin kayan masarufi na ‘kara hawa a kudu maso gabashin Najeriya, yayin da musulmi ke azumin watan Ramadan.
Gwamnatin jihar Abia ta ce tana iya bakin kokarinta wajen dakile barkewar cutar zazazabin Lassa a jihar, wadda ta yi sanadiyar mutuwar wata likita a wannan makon.
Shugban Najeriya Muhmmadu Buhari ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar bikin Easter, inda ya yi kira ga ‘yan kasar da su yi amfani da lokacin bikin su kaunaci juna da kuma gujewa duk abubuwan da ka iya tayar da zaune tsaye.
Miyetti Allah kungiyar Fulani makoyaya ta fito karara a jihar Imo, daya daga cikin jihohin kudu maso gabas ta karyata rade-radin cewa kungiyar na shirin kaiwa jihohin hari lamarin da shugaban kungiyar Alhaji Gidado Sadique ya ce shati fadi ne kawai.
Yayin da wasu 'yan yankin kudu maso gabashin Najeriya ke fadin cewa sun gwammace su ci gaba da zama a cikin Najeriya idan za a shimfida adalci a kasa, wasu cewa suke yi ko ba dade ko ba jima kasar Biafra zata tabbata