Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Taya Kiristoci Murnar Bikin Easter


Shugaban mabiya darikar katolia na duniya, Paparoma Francis
Shugaban mabiya darikar katolia na duniya, Paparoma Francis

Shugban Najeriya Muhmmadu Buhari ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar bikin Easter, inda ya yi kira ga ‘yan kasar da su yi amfani da lokacin bikin su kaunaci juna da kuma gujewa duk abubuwan da ka iya tayar da zaune tsaye.

Kakakin gwamnatin Najeriya, mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaba Buhari yana cikin murna da farin cikin taya ‘yan uwa Kirista murnar bikin Easter.

Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya Musulmai da Kirista wajen daukar kyawawan darasi na Annabi Isah (A.S), kuma ya yi fatan cewa za a yi amfani da wannan dama wajen nuna soyayya ga juna a kuma guji munanan kalamai da tsauraran ra’ayi da ke jawo fituna a kasa.

Sannan kuma shugaban ya yi amfani da wannan rana wajen yin godiya ga al’umomin daban-daban da ke bayar da gudunmawa wajen yaki da ta’addanci da sauran fituntunu da ke faruwa a kasa.

A wata takardar da babban limamin darikar Katolika a jihar Imo, Anthony Obinna, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu kishin gaskiya, domin lokacin Easter lokacin nasara ne, su kuma kubutar da kansu daga mulkin kama karya.

Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG