Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zabe A Jihar Imo


Taron jam'iyar PDP
Taron jam'iyar PDP

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta ayyana tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, a matsayin wanda ya lashe zaben gwanan jihar Imo.

Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP ya samu nasara ne da kuri'u 273, 404, yayin da Mista Uche Nwosu na jam'iyyar Action Alliance (AA) ya biyo shi da kuri'u 190, 364. Sanata Ifeanyi Araraume na jam'iyyar APGA ya samu kuri'u 114,676, a inda Sanata Hope Uzodinma na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 96,458, yayin da tsohon gwamnan jihar, Mista Ikedi Ohakim na Accord Party ya samu kuri'u 6,864.

Yanzu jama'a da dama suna ganin cewa wannan nasarar da Ihedioha ya samu, na zuwa ne a daidai lokacin da jahar Imo ke matukar bukatar ingantacciyar gwamnati da sabuntawa da kuma ci gaba, musamman a fannonin kayayyakin more rayuwa, da kasuwanci, da noma, da kiwon lafiya, da kuma samar wa al'umma abin yi.

Da yake tsokaci game da sakamakon zaben Dakta Celestine Nwosu wani malamin jami'a yace, "Nasarar da Emeka Ihedioha ya samu nasara ce ga al'ummar jihar Imo. Nasarar ta kubutar da Jahar Imo daga hannun wani mugun sarki. Gaskiya a matsayina na dan asalin jahar Imo, kamar an sauke min nauyi ne. Kuma mun godewa Allah cewa an kammala zaben lami lafiya."

Wata matashiya, Cynthia Ukah ita kuma cewa tayi, "Ina matukar farin ciki da ya ci zaben. Nasarar ta dace dashi, kuma galibi al'umma sun zabeshi. Sai dai ina so in shawarce shi cewa ya fi mayar da hankali kan samarwa mutane abin yi, saboda al'ummar jihar Imo suna matukar bukatar sana'o'in da zasu inganta rayuwarsu."

"Ina farin ciki sosai da cewa an yi zabe na gari, kuma ina farin ciki sosai cewa mutumin da al'umma sun zaba ne ya lashe zaben. Ina kira ga sauran 'yan takara da su hada karfi da karfe su mara masa baya don jahar Imo ta ci gaba," a cewar Prince Azubuike,

Ya zuwa lokacin tura wannan rahoton, ana ci gaba da bukukuwa da shagulgula, musamman a yankin Mbaise, inda ake murnar cewa wannan ne karo na farko da al'ummar jihar suka zabi dan Mbaise a matsayin gwamnan jihar.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG