Farfesa Ibrahim Ummate, jami’in cibiyar jinyar koda ta asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri a Najeriya, ya yi karin bayani a game da matsalar cutar koda da kuma kalubalen maganinta.
A Zambia, hukumomi sun ce ana samun karuwar matasa mata masu kamuwa da sankarar mama a kasar. Haka kuma, ana samun karuwar wadanda ake gano cutar a tare da su bayan ta kai mataki mafi muni a kurarren lokaci.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta kiyasta cewa mutane miliyan 850 ne suke fama da cutar koda a fadin duniya, sannan cutar ta na sanadiyyar mutuwar sama da mutum miliyan 2 da dubu dari shida a kowace shekara.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce “dole a kare” asibitocin da ke cikin Gaza, yayin da sojojin Isira’ila ke ci gaba da auna cibiyoyin lafiya a wannan yankin kasar ta Falasdinawa, bisa zargin cewa Hamas na rabewa da su.
Wannan na zuwa ne wattani 2 bayan da gwamnatin kasar ta janye matakin gaggawar lafiyar al’umma wanda aka ayyana tun shekarar 2022.
Kazalika Dr. Fatima Aliyu Magaji, ta yi bayyani a game da yadda matasa jakadun GREAT GREEN WALL suke daukan darussa daga wasu kasashen domin samun irin nasu mafita da za su dace da matsalolin da kasashen suke fama da su.
Wani kwararen likita a Najeriya, Dr Ibrahim ya yi karin haske a game da fida da mutum-mutumi.
A Afirka ta Kudu, an rungumi amfani da mutum-mutumi a aikin tiyata a zaman wani abin dogaro da shi nan gaba a fannin kiwon lafiya.
LAFIYARMU: Wani rahoto da kungiyar assasa ci gaba ta kasa da kasa, wato Global Action For Sustainable Development ta fitar a bana, ya ce kaso mai yawa na al’ummar Liberia na salwanta sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi.
A Afirka ta Kudu, an rungumi amfani da mutun-mutumi a aikin tiyata a zamanin wani abin dogaro a gaba a Fanin kiwon lafiya.
Yayin da sojojin Myanmar suke ci gaba da yaki da 'yancin fadi sonka, sojojin kasar ta Myanmar, sun bayyana kama wani tsohon ministan yada labarai a kasar.
China ta sanar cewa shugabancin jam'iyyar kwaminis na da mahimmiyar rawar da zai iya takawa a game da al'amuran kudade, a wurin babban taron da aka shirya don tattauna batutuwan da suka shafi samar da kudade da kuma kashe su wanda akayi a babban birnin kasar, Beijing
Amurka Ta Kara Tura daruruwan dakarunta a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Shirin ya mafia hankalo kan kafewar jinin al’ada na mata wato menopause da kuma daukewar sha’awa da kwayoyin haihuwa a maza wato Andropause.
Ana danganta kafewar jinin haila wato menopause da yawan jin zafi, gumi, yawan fushi da kuma sauyin lokacin saukar jinin al’ada. Andropause anayi ne da ake masa la’abi da “menopause din maza” wanda kehaifar da gagarumin sauyi a yanayin daidaituwar sinadarin hormones da kuma lafiyar jikin maza.
Duk da irin darajar da Allah yayi wa mace, takan tsinci kanta cikin kalubale, lamarin da ya kan kai ga ta fada cikin mummunan yanayi sakamakon irin raunin da take da shi.
Kungiyar UNESCO ta ce Afirka na ci gaba da fuskantar kalubalen karancin malamai a makarantu da dama sakamakon Karin masu nemar illimi sannan, da karancin wadatattun kayayyakin aikin da za su taimaka wajen inganta fannin illimi.
Shirin lafiyarmu na wannan makon, ya mai da hankali akan cututtukan Kansar da suka fi addabar mata a fadin duniya.
Domin Kari