Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciwon 'Ya Mace: Muhimmancin Neman Na Kai, Oktoba 25, 2023


Aisha Mu'azu
Aisha Mu'azu

Duk da irin darajar da Allah yayi wa mace, takan tsinci kanta cikin kalubale, lamarin da ya kan kai ga ta fada cikin mummunan yanayi sakamakon irin raunin da take da shi.

Shirin ya duba abubuwan da suka kamata a kiyaye don tabbatar da cewa mata suna samun na kashewa ba tare da an tauye hakkin zamantakewa ba ko kuma zubar da darajar ‘ya mace, wacce a kullum take fuskantar kalubale a duk lokacin da wani lamari mara dadi ya faru.
Zauren ya kuma karbi bakuncin Hajiya Fatima Muhammad Uwatara, wacce ake wa lakabi da Malama Dangana; malamar addini, ‘yar kasuwa kuma shugabar wata makaranta da ake kira ''Malama Dangana International school" a Ghana, da kuma Hajiya Sa’adatu Ala Kurawa, ma’aikaciyar jiyya mai ritaya, mai aiki da al’umma kuma mai aikin sasanta tsakani.

Alatsa nan don a saurari cikakken shirin:

CYM EP 183 - Mahimmancin Neman Na Kai.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:50 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG