Shugaba Biden yayi wannan furucin ne da yake amsa tambayoyi kan tabarbarewar al’amura a asibitin Al Shifa, wanda shi ne cibiya lafiya mafi girma a Birnin Gaza, wanda kuma sojojin Isira’ila ke ci gaba da yi masa kawanya a 'yan kwanakin kwanakin bayan nan. Al’amura sun tsaya cik a Al Shifa, saboda rashin makamashi, abinci, da ruwa.
Dubban majinyata da su ka matsu, sun gudu daga asibitin na Al-shifa a karshen makon da ya gabata, inda su ka bar sauran majinyata 650, da wasu dubban Falasdinawan, wadanda aka raba su da muhallansu, kana, suke neman mafaka daga wannan fadan.
Ma’aikatar Lafiyar Falasdinu, ta fada a ranar Litini cewa, majinyata 32 sun mutu a asibitin na Al Shifa, ciki har da wasu jarirai uku, tun bayan da aka yi wa asibitin kawanya, saboda rashin wutar lantarki.
Dandalin Mu Tattauna