Yayin da kasar China ke cigaba da fadada ayyuka a kasashen Afrika, a Najeriya wasu kamfanoni mallakar ‘yan kasar China na neman maida wasu 'yan gwangwan da masu kokarin kara sabunta wasu abubuwa su zama marasa aikin yi saboda yadda suka shiga sana’ar.
Babban Darekta Janar mai kula hukumar da dakile yaduwar cutar ta AIDS NACA Gambo Aliyu, yayi bayani a game da ci gaban da hukumar ta samu a yakin ta da cutar SIDA a Najeriya da ma kalubalolin da ake fuskanta na kyamatar masu cutar.
Kenya ta samu gagarumar ci gaba a yunkurin rage masu yawan kamuwa da cutar HIV cikin shekaru goman da suka gabata. An samu raguwar sabbin masu kamuwa da cuta da kaso 78% sannan an samu raguwar mutanen da AIDS yake sanadin mutuwar su da kaso 57%.
Cibiyar binciken al’amuran noma wato Institute of Agricultural Research ta jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ta samar da wani nau’in masarar da kwari basa ci mai suna TELA MAIZE. Ana fatar irin masarar zai taimaka wajen magance matsalar karancin girbi sakamakon kwari dake far ma gonaki.
Yayin da ake samun karuwar matsalar lalata da cin zarafi a Maiduguri, har ma a sansannonin ‘yan gudun hijira wasu kungiyoyin fafutukar mata suna bayyana damuwar su.
A Ghana, wani sabon kamfani ya samarwa gidaje da makarantu sauki bayan da ya kafa masu na’urar wutar lantarki mai amfani da hasken rana.
Shekaru 35 da suka gabata ne aka fara kebe ranar cutar SIDA ta duniya. An kebe ranar 1 ga watan Disamba na kowace shekara ne da zummar wayar da kai a game da cutar HIV da AIDS sannan a kuma masu fama da cutar a fadin duniya goyon baya.
Shirin da kasar take fata zai taimaka wajen bunkasa harkokin yawon bude ido da kuma tattalin arzikin kasar.
A bisa wani rubutu da aka wallafa cikin wata mujallar likitanci mai suna BMJ a 2020, rashin abinci ne ke sanadiyyar mutuwar daya cikin mutane 5 dake mutuwa, fiye da duk wani yanayi mai hadarin, har ma da taba.
Babban Malamin Addinin Musulunci kuma Jagoran Darikar Tijjaniyya, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ya bada gudummawar kudi Naira Miliyon dari (100) domin Taimaka wa Mutanen kasar Falasdinu da suke yaki da kasar Israila.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na ziyara a Jamus domin halartar taron hadin-gwiwar Kungiyar Kasashen nan 20 masu Karfin Tattalin Arziki ta G20 da Afirka.
Ana samun cutar koda ne asa'adda kodar mutum ta lalace yadda ba za ta iya tace jini da kyau ba. Galibi ba a iya gano cutar da farko, har sai bayan cutar ta ci karfin mutum, wanda galibi yakan bukaci wankin koda da aka fi sani da dialysis.
Farfesa Ibrahim Ummate, jami’in cibiyar jinyar koda ta asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri a Najeriya, ya yi karin bayani a game da matsalar cutar koda da kuma kalubalen maganinta.
A Zambia, hukumomi sun ce ana samun karuwar matasa mata masu kamuwa da sankarar mama a kasar. Haka kuma, ana samun karuwar wadanda ake gano cutar a tare da su bayan ta kai mataki mafi muni a kurarren lokaci.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta kiyasta cewa mutane miliyan 850 ne suke fama da cutar koda a fadin duniya, sannan cutar ta na sanadiyyar mutuwar sama da mutum miliyan 2 da dubu dari shida a kowace shekara.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce “dole a kare” asibitocin da ke cikin Gaza, yayin da sojojin Isira’ila ke ci gaba da auna cibiyoyin lafiya a wannan yankin kasar ta Falasdinawa, bisa zargin cewa Hamas na rabewa da su.
Wannan na zuwa ne wattani 2 bayan da gwamnatin kasar ta janye matakin gaggawar lafiyar al’umma wanda aka ayyana tun shekarar 2022.
Domin Kari