Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Ne Suka Hallara a Filin Times Square a New York Don Tarbar Sabuwar Shekarar 2024


Taron mutane a Timesquare
Taron mutane a Timesquare

NEW YORK (Reuters) Bayan kwashe tsawon sa’o’i masu yawa a tsaye a filin Times Square a birnin New York, dubban mutane cikin farin ciki suka yi maraba da shigowar sabuwar shekara a daren jiya Lahadi inda aka saba yin wasa don murnar shigowar sabuwar shekara.

Gwamman mutane ne suka isa filin tun da sanyin safiyar jiya Lahadi domin samun wurin da zasu baje kafin wurin ya yi cunkoso a wuraren da jami’an ‘yan sandan birnin New York suka sanya shingaye, gabanin mawaka Megan Thee Stallion da LL Cool J su rera wakoki kafin a fara kirga dakikai zuwa tsakar dare.

“wannan shine karo na farko da na hallarci bukin sabuwar shekara a filin Times Square a cewar Nadja Sjostrom mai shekaru 44, wacce ta taso tun daga Stockholm a kasar Sweden ‘yan kwanaki gabanin wannan rana kana tana tsaye a gaban manyan na’urorin yada hotuna da ke Times Square tun akalla karfe 8 na safe.

Ga mazaunin Brooklyn Markus Washington dan shekaru 49 kuwa, tafiyar tasa ta kasance ‘yar gajeruwa, sai dai kuma kamar Nadja, wannan shine karo na farko da zai hallarci bukin sabuwar shekarar a filin Times Square.

Yace, “Yana bani shauki yace. Abin ban sha’awa, akwai sanyi amma gaskiya da ban sha’awa.”

Markus ya kara da cewa, “tun sa’ilin da nake yaro karami, ina kalon bukukuwan a kafar talabijin sabo da haka na ce ya kamata ni ma ayi da ni. Ya ayyana bukin da wanda za ayi shi sau daya a rayuwa tare da jaddada cewa bashi da niyyar sake maimata wa.” Ina son New York amma tsayawa na sa’o’i 15 don ganin wannan bukin yayi tsawo”.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG