A wani cigaba a fagen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, runduanr sojin Najeriya ta ce ta aika da wasu 'yan kungiyar Bako Haram da dama zuwa lahira.
A cigaba da neman bakin zaren game da yawan shiga Turai da bakin haure ke yi, kasashen Turai za ku kafa wata runduna ta kula da zirga-zirgar jama'a a kan iyakoki musamman na wasu kasashe.
kamar yadda 'yan siyasa su ka saba yi, a najeriya, 'yan takarar da su ke ganin ba a masu adalci ba, na ta canza sheka daga wannan jam'iyyar zuwa waccan.
Yinkurin 'yan ta'adda na zurma al'ummar Fulanin Janhuriyar Nijar cikin harkar ta'addanci ya ci tura bayan da Fulanin su ka yi banza da zawarcin 'yan ta'addan.
A Gabon rashin cikaken bayanai akan lafiyar shugaban kasar Gabon Ali Bongo mai shekaru 59 da haihuwa wanda kuma yanzu haka yake kwance a asibiti Ryadh ya fara janyo cece kuce mai tada hankali a kasar.
A cigaba da yinkurinta na kare Janhuriyar Nijar daga illar 'yan ta'adda, Rundunar Sojin Janhuriyar ta Nijar ta kakkabe 'yan ta'addan da a baya su ke tayar da kayar baya a yankin kan iyakar Tilabery
Yayin da ake cigaba da farautar wasu da ake zargi da hannu a sacewa da kuma kisan Janar Idiris Alkali (murabus) a wani kauyen jahar Filato, an gano tare kuma da yin jana'aiza ma gawarsa a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.
Kamar yadda al'amarin ya ke a wasu jahohin Najeriya, jahohin Adamawa da Taraba na fama da matsalar sace mutane don nemar kudin fansa.
A Jamhuriyar Nijer 'yan adawa Sun fice daga zauren taron kwamitin da aka dorawa alhakin kwaskware kundin zaben kasar bayan da aka samu rarrabuwar kawuna akan wasu mahimman dokokin da ke kunshe a wannan kundi da 'yan hamayya ke yiwa kallon haramtacce.
A Janhuriyar Niger ne aka yi bikin nadin sarautar Abzin dogarawa a yankin birnin Tahoua dake Janhuriyar Niger. Basaraken ya abu na fari da zasu yi shine rokon Allah.
A Nigeria a karo na biyu da aka kwashe ana arangama, jami’an tsaro sun bude wuta akan Musulmi ‘yan Shi’a, wadanda ke tattakin neman a saki shugabansu a Abuja.
A Amurka kuma: Sakataran tsaron Amurka Jim Mattis ya yi kiran a tsagaita wuta a Yamen domin nuna goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya akan kokarin da take yi na kawo zaman lafiya.
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Jamhuriyar Nijar CSC Dr. Kabiru Sani ya nuna juyayi game da rasuwar Mariama Keita, tsohuwar shugabar hukumar ta Sadarwa, kuma macce ta farko da ta fara aikin jarida a Nijar.
Dakarun Najeriya sun budewa mabiya mazhabar Shia wuta yayin da suke tattakin neman a saki shugabansu El Zakzaky wanda hukumomi ke tsare da shi tun bayan da jami’an tsaro suka kashe daruruwan mabiyansa.
Daruruwn mutane sun yi gangami a wajen jana’izar wani bafalsadine dan shekaru 25 da dakarun Isra’ila suka kashe yayin wata zanga zanga a jiya Litinin.
Domin Kari