A kasar Senegal dubun dubatar jama’a mabiya Tarikar Mouride sun hallara a birnin Touba na Senegal domin halartar taron “Grand Magal” da mabiyansa ke yi shekara-shekara.
A yau ne jirgin kasar Indenosia na Lion Air dauke da mutane 189 ya fada cikin tekun tsibirin Java da ke Indonesia a yau Litinin mintina 13 bayan tashi daga filin jirgin Jakarta.
A cigaba da takaddama tsakanin sojojin Najeriya da 'yan mas'habar Shi'a, an kashe a kalla 'yan Shi'a biyu a wata arangamar da aka yi tsakanin bangarorin biyu a Abuja.
A Janhuriyar Nijar mai cike da al'adu iri-irir, an nada Sarkin Dogarawan Abzin a wani kasaitaccen da ya burge masu wannan al'adar da kuma 'yan kallo.
A cigaba da tashe-tashen hankula a yankin arewa maso gabashin Najeriya, wasu makasa, wadanda ba a san ko su waye ne ba, sun dira wata sabuwar kasuwar dabbobi, inda su ka yi wata kazamar barna.
A cigaba da yaki da safarar mutane da muggan kwayoyi da ta ke yi, Janhuriyar Nijar ta lashi takobin ganin bayan masu aikata wadannan manyan laifuka a kasar.
A Najeriya shugaban ‘yan gwagwarmayar kabilar IPOB Nnamdi Kanu, ya yi jawabi a rediyo a ranar Lahadi inda ya ce yana kasar Isra’ila. Rabon da a ji duriyarsa tun a watan Satumbar bara.
A yau Talata ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya gabatar da wasu bayanai da suka saba wanda Saudiyya ta fitar kan kisan Khashoggi inda ya nemi da a hukunta duk wanda ke da hannu
A kasar an bude wani sabon kanfanin motocin Taxi mai suna An Nisa ya fara aiki don anfanin mata zallansu kawai, don tsaron lafiya, jin dadi da rufin asiri gare su.
A Brazil duban mutane ne suka yi zanga-zanga a tittunan manyan biranen kasar domin nuna kin amincewarsu da takarar babban dan siyasa Jair Bolsonaro, kasa ga mako daya kafin zagaye na biyu na zaben da za’ayi ran 28 ga watan nan na Oktoba.
Wata kotun sojin Najeriya ta yanke hukunci ga wasu jami'anta shida, ciki har da jami'in da aka yanke masa hukuncin kisa.
Hadakar kungiyoyin Timidria da ke yaki da bauta a Nijar ta fitar da sanarwar nuna goyon bayan Adam Biram Dah Abeid da hukumomin Mauritaniya suka tsare.
A cigaba da kokarinta na yaki da bauta a Janhuriyar Nijar da makwabtan kasashe, kuniyar yaki da bautar da mutane, Timidria, ta lashi takobin kai wani batu na bautar da wata mace ga kotun CEDEAO.
A wani yunkuri na kwantar da hankalin jama'a da rundunar 'yan sandan jihar Filato ta sha alwashin yin aikinta babu sani ba sabo dangane da bacewar Janar Idris Alkali.
A cigaba da kokarin farfado da ayyukan noma da kuma raya kogin Naija (ko kuma Nijar), kasashen da ke cin moriyar wannan kogin sun zaburo don tattalin albarkatun kogin da ma kogin kansa.
Himma Ba Ta Ga Rago
Domin Kari