Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar yin nasarar kakkabe ‘yan ta’adda daga wuraren da suke da galaba a yankin Tilabery sakamakon wani gagarumin farmakin da dakarun kasar ta Nijar suka kai a kwanakin nan a yankunan da ke iyaka da Burkina Faso.
A yayin da ya ke yi wa majalisar dokokin kasa bayani a dangane da halin da ake ciki a yankin Tilabery, biyo bayan rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga na karbar kudaden haraji tare da fitar da zakka daga dukiyoyin wasu makiyayan dabobi a yankin ne Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohammed ya sanar cewa dakarun tsaron kasar da ke karkashin rundunar musamman ta mayakan Nijer da ke da mazauni a kauyen Torodi ta yi nasarar wargaza wuraren da ‘yan ta’adda suka kafa sansani.
Mutane kimanin 17 ne ‘yan bindiga suka hallaka a garin inates sai kisan hakimin Gasa lokaci guda da wani farar hula da aka kashe a Ayoru ba’idin yawaitar sace sacen daruruwan dabobi da koke konen makaratun boko laifin da ake dora alhakinsa a wuyan ‘yan ta’ddan Mali
Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum