A Jamhuriyar Niger, a wani taro da aka yi a birnin Yamai, kungiyar raya kasashen Afrika ta yamma da ake kira ECOWAS ko CEDAO a takaice, ta kuduri aniyar aiki da matasa wajen samar da zaman lafiya da kuma yaki da tsattsauran ra’ayi.
US: Adadin mutanen da suka mutu a wutar dajin California ya kai 83 bayan da aka samu karin wasu mutane biyu da wutar ta rutsa da su a ranar Laraba. Yanzu haka an shawo kan kashi 85 cikin 100 na wutar.
A Faransa majalisar ‘yan sandan kasa-da-kasa ta zabi Kim Jong Yang dan asalin kasar Korea ta kudu a matsayin sabon shugaba a yau Laraba.
Afrika ta kudu, wata kungiyar mai suna Afriforum da ke wakiltar kashi biyar cikin 100 na mutanen da asalinsu ‘yan Holland da Jamus da Faransa ne, ta kara kaimi wajen yin zanga zanga kan tsarin raba filaye.
Kamar yadda siyasa ta gada, bayyana sunayen 'yan takara ke da wuya sai aka shiga jayayya kan sunayen a wasu jahohin da su ka hada da Adamawa
A wani yinkuri na neman sanin samfur din yanayin gidaje a Janhuriyar Nijar, hukumar kidaya za ta dau alkaluma a dubban gidaje a wurare wajen 250 a kasar.
A cigaba da kokarin da kasashe ke yi na tsaftacce muhalli, wasu sassan Janhuriyar Nijar sun mai da hankali kan kawar da ledoji.
A karon farko, Shugaban Gabon, Ali Bongo ya bayyana cewa yana fama da matsananciyar rashin lafiya bayan da ak kwantar da shi a asibiti har na tsawon makonnni uku a Saudiyya, ko da yake, rahotanni sun ce yana samun sauki.
Dakarun Isra’ila sun kai wasu hare-haren da suka ce na martani ne a yankin zirin gaza, bayan da aka harba rokoki a yankunansu.
Domin Kari