Ma'aikatar kididdiga ta Nijer reshen jahar Dosso, ta gudanar da taron fadakarwa, da ya hada hukumomi na birane da sarakunan gargajiya da limamai da manyan malamai, on samo wata kididiga ta iyalai daban - daban gameda halin rayuwarsu domin tantance wadanda ke cikin matsanancin talauci domin su kansu, su dauki matakan kyautata rayukansu da irin yanda hukumomin kasar ke iya agaza musu.
Magatakardan offishin gwamnan jahar Dosso Malam Assumane Amadu shine ya jagoranci bukin soma wannan taron a Birnin Dosso, kuma a lokacin da yake jawabin soma taron yana mai cewa za a yi wannan aikin ne saboda amfanar jama'a. Don haka ya bukaci hadan kan jama'ar.
Labarun da ke gare mu a halin yanzu, sun nuna cewa tsawon wadannan watanin 3, tawagogi 15 na ma'aikatar kididdiga ta wannan kasar kowace da durobanta da shugaban tawagar da masu kididiga 3 za su ziyarci dukkan fadin Nijer domin tantamnawa da iyalai dubu 3 a wurare 250 a dukkan fadin Nijer.
Ga wakilinmu a Birnin Konni Harouna Bako da cikakken rahoton:
Facebook Forum