Shiyya ta uku ta da'irar Damagaram ta kaddamar da wani shiri na sayen ledodi,a karkashin tallafin shirin projet PRO-EMPLOI da kungiyar GIZ ta kasar Jamus ta bullo da shi. Kimanin mutane dari biyu da hamsin ne aka zaba da suka hada da mata masu karamin karfi, mabukata da matasa marasa aikin yi, inda za a biya su jika tamanin na sefa tsawon kawna arba'in, wanna shiri zai taimaka wajen tsabtar muhalli da yaki da hamada,
Ance kimanin mutun dari biyu da hamsin aka zaba wadanda suka hada da mata dari da saba'in da maza tamanin su ka yi aikin tsinar ledar da suka kai shiyyar ta uku, inda ko wannensu zai samu jikka tamanin ta sefa (F.CFA)
Wasu mata Hadiza, Rabi da Mariama da suka kawo ledodni sun ce wannan ba karamin taimaka musu aka yi ba, inda suka ce kudin nan zai shafe musu matsaloli da dama musamman na abinci da makarantar yara.
Facebook Forum