Fira Ministan Mali, Soumelou Boubeye Maiga da ministocinsa sun yi murabus jiya Alhamis, ya yin da ake ci gaba da samun tashin hankali a kasar.
A Sudan Dubban masu zanga-zanga sun fito kan tituna a Khartoum suna bukatar majalasun sojoji so mika hanzarta mulki wa farar hula jiya Alhamis
A Ivory coast, Ivanka Trump, diyar shugaban Amurka Donald Trump, ta halarci wani taron kolin mata ‘yan kasuwa na yankin Afrika ta yamma da aka yi karon farko.
Hukumar kwastan dake kula da shiya ta daya a legas ta kama kayan sumogal na fiye da Naira Biliyan Biyu da suka hada da muggan kwayoyi a cikin watanni 3 da suka gabata.
Hukumomin shari'a a jamhuriyar Nijer Sun sallami wasu dalibai kimanin 100 wadanda jami’an tsaro suka cafke a yayin wata zanga zangar da daliban suka gudanar a ranar 9 ga Watan Afrilu a birnin yamai.
TASKAR VOA: A Najeriya, Hukumar Samar Da Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya FAO Ta Kaddamar Da Wani Shiri Na Noman Kifi A Garin Maiduguri
Shguaban Amurka Donald ya kujerar naki kan dokar da Majalisa ta amince da ita, wadda za ta kawo karshen taimakon da Amurka ke baiwa Saudiyya a yakin da take jagoranta a Yemen
A Masar, mafi yawan ‘yan Majalisa suka amice da dokar da za ta baiwa shugaban kasa Abdel Fattah al-Sisi damar yin mulki har sai shekarar 2030. Al-Sisi dai ya kasancew kan mulki tun tun 2013 bayan tunbuke zababbben shugaban kasa Mohammed Morsi.
Hukumomin Jamhuriyar Nijer Sun damke wani dan kasar mai suna Ali Tera mazaunin Amurka domin ya gurfana a gaban kuliya sakamakon wasu tarin laifukan da ake zarginsa da aiktawa.
A cikin shirin Taskar VOA na wannan makon, zaku ga sakon iyayen sauran daliban makarantar Chibok da har yanzu ke hannun ‘yan Boko Haram, ga gwamnatin Najeriya.
Manyan jami’an gwamnatin kasar Nijer da wakilan cibiyar raya kasashe masu tasowa ta Amurka da ake kira Millennium Challenge of Cooperation da truancy sun kai ziyara a birnin Konni, da zummar duba hanyoyin farfado da madatsar ruwan Muzage don noman rani.
Gobara ta lake rumfunan 'yan gudun hijira 232, a wani kauyen sajeri dake muna ta jihar Borno a cewar hajiya Yabawa Kolo, shugabar hukumar SEMA.
Jiragen yakin Najeriya da Nijar na can na ci gaba da bude wuta akan mayakan boko haram a yankin tafkin tchadi.
Hukumar Zaben Jamhuriyar Nijer Ta Bayyana Shirin Fara Rajistar Sunayen ‘Yan Kasar Mazauna Kasashen Waje A Zaben shekarar 2021. da nufin tantance wadanda suka cancanci kada kuri’a a zabubukan 2020 da 2021.
‘Yan Majalisu a Sudan sun amince da dokar ta baci ta tsawon watanni shida, maimakon ta shekara daya da shugaba Omar al-Bashir ya ayyana domin kawo karshen zanga-zanga.
Ga tattaunawar Abdoul’Aziz Adili Toro da ya yi da Grace Alheri Abdu da ta je Najeriya musamman domin hidimar zaben shugaban kasar 2019 da na ‘yan majalissar tarayya da aka yi a watan da ya gabata
Domin Kari