A Jumu’ar nan ma, masu zanga-zanga sun sake taruwa a a Algeria, suna zanga-zangar neman shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya yi murabus.
Kwamandan rundunar sojojin Amurka dake nahiyar Afirka, ya fadawa ‘yan Majalisun Amurka cewa bashi da tabbacin ko Pentagon za ta iya rage kashi 10 cikin 100 na yawan sojojin Amurka dake Afirka kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar a shekarar da ta gabata.
Faransa: A yau Alhamis ne wata kotu ta kama wani babban jigon cochin Katolika Cardinal Philippe Barbarin da laifin kin bayyana zargin gallazawa ta jima’i da akayi wa wani Fada na cocin Katolika.
Najeriya: Akalla mata takwas daga mata kimanin 2,000 da aka baiwa katin gayyatar kallon gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka yi a Rasha suna ikirarin cewa an tilasta musu zama karuwai jim kadan bayan isa Moscow
Babban hafsan sojojin Algeria Janal Ahmed Gaid Salah, ya ce masu zanga-zangar kin jinin shguaban kasa Abdelaziz Bouteflika, mutane ne da ke son dawo da rashin zaman lafiya Algeria.
A wani sabon rahoton kungiyar kare hakkin bil Adama ta Huram Right, hukumomin tsaron Iraqi sun kama daruruwan kananan yara da shekarunsu basu wuce 14 ba, ana azabtar da su tare da ajiye su a gidan Yari kan zargin da ake musu na alaka da mayakan IS
Hukumar kiwon Lafiya a Jamhuriyyar Nijar zata kaddamar da shirin riga kafin Cutar Sankarau, ga yara kanana fiye da Miliyan 6, na tsawon mako daya daga gobe Talata a duk fadin kasar. Biyo bayan wani rahoto da ya tabbatar da bullar cutar a jihar Damagaram.
Ga wasu daga cikin hotuna bidiyon da wakillanmu suka yi a lokacin da ake zabe ta shafin Facebook kano, Abuja, Katsina, Adamawa da puma Jos.
A Amurka shugaba Donald Trump yace shadai da tsohon lauyansa Michael Cohen ya gabatar ga ‘yan Majalisar Dokoki ta taimaka wajen hana samun nasarar taron da ya yi da shugaban kasar Koreya ta Arewa Kim Jon Un.
A ksar Masar an sako dan jaridar daukar hotuna Abou Zaid, wanda aka fi sani da lakabin Shwakan, daga gidan kurkuru a yau litinin ya kuma ya koma gidansa. Tun a shekarar 2013 aka kame wannan shahararen dan jarida da ya sha samun lambobin yabo na aik
Najeriya: A wani bincike da hukumar kididdiga ta Najeriya da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF su ka yi, ya nuna cewa miliyoyin ‘yan Najeriya ba sa samun tsaftatacen ruwan sha.
Isra'ila: Shugaban kasar Liberiya George Weah, ya gana da shugaban Isra'ila Reuven Rivlin a birnin kudus ya kuma ya jaddada cewa kasarsa na "shirye don huldar kasuwanci" da Isra'ila.
Vietnam: Shugaban kasar Amurka Donald Trump na kan hanyarsa ta dawowa Amurka daga Hanoi bayan da ganawarsa ta biyu da shugaban KTA, Kim Jong Un, ta kere ba tare da cimma wata yarjejeniyan ba.
Shugaban kasar Nijer ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari sakon taya murna sakamakon lashe zaben da akayi a kasar. Mahamadu Isuhu ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata dama da za ta baiwa gwamnatocin kasashen 2 sukunin ci gaba da aiyukan hadin guiwa tsakaninsu.
Kwana daya kenan bayan da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi takardar shaidar cin zabe a karo na biyu daga hannun shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakubu.
Yan Najeriya Mazauna Nijar sun bayyana ra'ayoyinsu game da nasarar da shugaba Mahamadu Buhari ya samu a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Domin Kari