Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Girke Jami'an Tsaro A Jihar Adamawa Don Zabe


Tun da sanyin safiyar yau ne jami’an zabe suka isa rumfunan da za’a yi zabe a jihar Adamwa yayin da aka baza jami’an tsaro don shirin ko ta kwana, ko da yake a wasu wuraren jama’a basu fito sosai ba.

Wasu da suka kada kuri’arsu sun bayyana yadda zaben ya wakana da kuma fatansu ga wanda zai zama gwamna.

Kafin a dakatar da zaben sakamakon dabubuwan da suka faru da farko, dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, Ahmadu Umaru Fintiri ne ke kan gaba da kuri’u dubu dari uku da sittin da bakwai, da dari hudu da saba’in da daya, yayin da gwamnan jihar dan jam’iyar APC Sanata Muhammmadu Bindow Umaru Jibrilla ke da kuri’u dubu dari uku da talatin da hudu da dari tara da casa’in da biyar, wato rattar dake tsakanin su kusan dubu talatin da biyu da dari hudu da saba’in da shida, wanda kuma yanzu lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda zata kaya a zaben na yau.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG